Bakonmu A Yau

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 1:31:43
  • More information

Informações:

Synopsis

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Episodes

  • Mubarak Abdul-Aziz kan ci gaban da ake samu a tattaunawar Amurka da Iran

    27/05/2026 Duration: 03min

    A daidai lokacin da ake kan tattaunawa tsakanin Iran da Amurka don samar da yarjejeniyar kawo ƙarshen yakin da ake yi tsakaninsu, kafafen yaɗa labaran Iran sun ce akwai gagarumin cigaba a tattaunawar. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Malam Mubarak Abdul-Aziz, ɗan Najeriya mazauni Tehran, wanda ya yi masa ƙarin bayani a game da halin da jama’a ke ciki daidai wannan lokaci da ake dakon cimma yarjejeniya don kawo ƙarshen wannan yaƙi. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Tattaunawa da Dr. Nasiru Sani Gwarzo kan sake ɓullar cutar Ebola

    26/05/2026 Duration: 03min

    Jami’an Lafiya na ci gaba da ƙoƙarin daƙile yaɗuwar cutar Ebola da ta sake ɓulla a Jamhuriyar Congo, wadda kawo yanzu ta shiga maƙwafciyarta Uganda. Zuwa wannan lokacin dai, cutar wadda a wannan karon ta bayyana da wani sabon nau’in, ta laƙume rayukan mutane fiye da 100, yayin da wasu kusan dubu ɗaya suka kamu. Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Nasiru Sani Gwarzo ƙwararre kan fannin kiwon lafiya da daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, wanda ya yi tsokaci kan dalilan da suka sa wankin hula ke neman kai wa dare. Ku latsa alamar sauti domin sauraron tattaunawarsu....................

  • Hon Ishaq Muktar Yakasai kan zaɓukan fiddan gwana na jam'iyar APC

    25/05/2026 Duration: 03min

    A Najeriya jam’iyyar APC mai mulki ta kammala zaɓen fitar da ƴan takara a dukannin matakai, inda a ƙarshe magoya bayan jam’iyyar suka amince da Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda zai sake tsayawa takarar shugabancin ƙasar a shekara mai zuwa. An dai samu ƙorafe-ƙorafe da kuma taƙƙadama a tsakanin ƴantakara, ya yin da wasu ke zargin cewa an yi musu ba daidai ba.  Abdoulkarim Ibrahim Shikak ya zanta da Hon Ishaq Muktar Yakasai, magoyi baya jam’iyyar ta APC kuma wanda ya taka wara domin haɗa kan magoya baya a lokacin zaɓukan. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu............

  • Tattaunawa da masanin doka kan hukuncin kotu game da jadawalin INEC

    22/05/2026 Duration: 03min

    Kotu a Najeriya ta yi hukunci da ke cin karo da umarnin hukumar INEC da ta nemi dukkanin jam’iyyun siyasa su kammala miƙa mata sunayen ƴan takarar da suka tsaida kafin nan da ranar 31 ga watan da muke na Mayu, duk kuwa da tanadin dokar zaɓen ƙasar da ta sahalewa jam’iyyun kaiwa har nan da watan Satumba gabanin miƙa sunayen. Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawar Abdoulkarim Ibrahim Shikal da masanin doka a Najeriya Barista El-zubair Abubakar kan wannan hukunci....

  • Tattaunawa da Farfesa Umar Pate kan cikar RFI Hausa shekaru 19 da kafuwa

    21/05/2026 Duration: 03min

    A wannan Alhamis 21 ga watan Mayu, Sashin Hausa na Radio France International RFI ke cika shekaru 19 da kafuwa, bayan fara yaɗa shirye-shiryensa a shekarar 2007, kuma dangane da wanna rana Nura Ado Suleiman ya tattauna da Farfesa Umar Pate, ɗaya daga cikin masanan da ke bibiyar ayyukan wannan kafa a Najeriya.

  • Hajiya Fatsuma Adamu shugabar makarantar da Boko Haram ta sace ɗalibai a Askira-Uba

    20/05/2026 Duration: 03min

    Gwamnan jahar Borno Babagana Umara Zullum ya ce, gwamnati da jami’an tsaro na ƙoƙarin ceto daliban makaranta da aka sace a makarantar firamare a ƙauyen Mussa dake ƙaramar Hukumar Askira- Uba. Gwamna Zulum ya bayyana haka ne ya yin wata ziyarar jaje da ya kai Askira Uba dangane da iftila’in da ake dangantawa da Boko Haram. Ziyarar na zuwa ne yayin da aka shiga kwanaki na 5 da sace daliban ciki harda kanan yara. Shugabar kula da ilimi na ƙaramar Hukumar Askira-Uba, Hajiya Fatsuma Adamu Askira ta bayyana mana halin da ake ciki, a tattaunawarta da Ahmad Abba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.

  • Tattaunawa da Dakta Nasiru Sani Gwarzo kan giɓin kasafin da WHO ke fuskanta

    19/05/2026 Duration: 03min

    Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta fara babban taronta karo na 79 jiya Litinin a birnin Geneva, wanda kuma za a ƙarƙare shi a ranar 23 ga watan Mayu da muke. Daga cikin muhimman batututwan da taron zai fi mayar da hankali a kai dai akwai giɓin kasafin kuɗin da ya kai Dala Biliyan 1 da Hukumar Lafiyar ta Duniya ke fuskanta, da kuma tasirin janyewa daga cikinta da Amurka ta yi. Kan wannan da kuma sauran batutuwa masu alaƙa, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Nasiru Sani Gwarzo, ƙwrarre kan sha’anin lafiya da ke Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.

  • Dr Kabiru Adamu kan kisan jagoran ƙungiyar IS Abu Bilal Al-Minuki

    18/05/2026 Duration: 03min

    Yanzu haka na ci gaba da bayyana ra’ayoyi dangane da sanarwar da Amurka ta fitar da ke cewa ta kashe Abu Bilal Al-Minuki da ke matsayin jagora a ƙungiyar IS a Najeriya, labarin daga bisani hukumomin tsaron Najeriya suka tabbatar. To domin jin ƙarin bayani a game da wannan ɗan taliki da ake cewa an kashe, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Dr Kabiru Adamu na Cibiyar da ke nazari kan sha’anin tsaro ta Beacon da ke Abuja, ga kuma zantawarsu. Ku latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar...............

  • Zantawa da Macron a ƙarshen taron ci gaban Afirka

    14/05/2026 Duration: 10min

    A zantawarsa da Radio France Internationale, da France 24 da kuma TV5 Monde a ƙarshen taron Afrika da Faransa da aka kammala birnin Nairobi na ƙasar Kenya, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana matsayinsa a game da taɓarɓarewar sha’anin tsaro a Mali da kuma alaƙar Faransa da sauran ƙasashen Afirka ta fannin tsaro da aikin soji. To amma da farko shugaban ya fara amsa wata tambaya ce dangane da dalilan da suka sa Faransa ke ci gaba da taka rawa a wajen tafiyar da takardar kuɗin CFA. Ga dai tattaunawar. Latsa alamar sauti domin sauraren zanatawar.

  • Sanata Abubakar Kyari kan makomar noma a Najeriya

    13/05/2026 Duration: 03min

    A ranar Talata ne ake kammala taron shugabannin ƙasashen Afirka da Faransa da ya gudana a birnin Nairobi ta ƙasar Kenya, wanda ya mayar da hankali kan hanyoyin ci gaban tattalin arziki da noma da samar da abinci ga jama'ar nahiyar. Yaƙin Iran na ɗaya daga cikin abubuwan da ake ganin na maida hannun agogo baya wajen  magance ƙarancin abinci, musamman rufe mahsigin Hormuz da ake amfani da ita wajen safarar takin zamani. Kan haka ne Nura Ado Suleiman ya zanta da ministan noman Najeriya Sanata Abubakar Kyari a wurin wannan taro, inda kuma ya ce su na ƙoƙarin magance matsalar. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Abubuwan da taron Faransa da ƙasashen Afirka ke son cimma

    12/05/2026 Duration: 03min

    A jiya ne ake faro taron kwanaki biyu tsakanin Faransa da ƙasashen Afrika a birnin Nairobi, wanda shugaba Emmanuel Macron da takwaransa William Ruto ke jagoranta. Taron ya haɗa shugabannin ƙasashen Afrika, da Hamshaƙan ƴan Kasuwa, da sauran masu ruwa da tsaki domin tattaunawa kan nemawa nahiyar Afrika mafita wajen samun ci gaban Tattalin Arziƙi  a fannonin da suka haɗa da, bunƙasa Masana’antu da Kimiyya da Fasaha da inganta Noma da Tsarin Kiwon Lafiya, da kuma samun wadatar makamashi. Danna alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar Nura Ado Suleiman da hadimin  shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Daniel Bwala.......

  • Boubacar Ɗan Zourmani akan makasudin ƙafa kungiyar ƙawancen ADS

    11/05/2026 Duration: 03min

    A ranar asabar da ta gabata ne, wasu masu fafufutuka da suka haɗa da ƴan siyasa, fararen hula, masana dokoki da dai sauransu da ke zaune a ƙetare, suka ƙaddamar da wani ƙawance da ake kira da suna ADS, (Alliance des Domocrates du Sahel) wanda babbar manufarsa ita ce sake dawo da tsarin dimokuraɗiyya a ƙasashen yankin Sahel da yanzu haka ke ƙarƙashin mulkin soji da suka hada da Burkina Faso, Mali da kuma Nijar. An dai ƙaddamar da wannan ƙawance ne a birnin Brussels na ƙasar Belgium, inda daga bisani Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Sakataren Yaɗa Labarai na ADS Boubacar Ɗan Zourmani, wanda ya yi masa ƙarin bayani a game da manufofinsu. Ga dai ƙarin bayaninsa.

  • Tattaunawa kan ci gaba da shari'ar neman hana Jonathan tsayawa takara a Najeriya

    08/05/2026 Duration: 03min

    Kotu a Najeriya yau ta ci gaba da sauraron shari'ar neman hana tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan tsayawa takarar zabe mai zuwa, kwana guda bayan wasu tarin magoya bayan sa sun bukaci ya shiga zaben mai zuwa. Dangane da matsayin dokar zabe a kan takarar ta Jonathan masanin shari'a, Farfesa Shehu Abdullahi Zuru na Jami'ar Baze dake Abuja, ya mana tsokaci a kai yayin zantawarsa da Bashir Ibrahim Idris. Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...

  • Ambasada Kazaure kan kiran wasu ƴanmajalisar Najeriya na kwace lasisin MTN da DSTV

    07/05/2026 Duration: 03min

    Wasu daga cikin Ƴan Majalisun Dattawan Najeriya sun buƙaci ɗaukar matakai maus tsauri a kan Afirka ta Kudu, ciki harda kwace lasisin kamfanonin su na MTN da DSTV saboda yadda ake kai wa ƴan ƙasar hari ake kuma kashe su. Majalisar ta yanke hukuncin tura tawaga Afirka ta Kudu domin tattaunawa da hukumomin ƙasar, yayin da shi ma bangaren gwamnati ya tura ministan harkokin waje. Ambasada Ibrahim Kazaure, tsohon Jakadan Najeriya a Saudi Arabia ya yi tsokaci a kai, a tattaunawar su da Bashir Ibrahim Idris.

  • Hira da Kailani Muhammad kan baiwa China ragamar farfaɗo da matatun man Najeriya

    06/05/2026 Duration: 03min

    Kamfanin mai na NNPC ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da wasu kamfanonin ƙasar China guda biyu, Sanjiang Chemical Company Limited da kuma Fuzhou Industrial Park, domin farfaɗo da matatun mai na Warri da Port Harcourt. Wannan mataki ya zo ne bayan matatun man sun laƙume kimanin biliyan 3.2 na dala ba tare da an samu biyan buƙata ba. Injiniya Kailani Muhammad, tsohon babban jami’in kamfanin na NNPC ne, a tattaunawarsa da Shamsiyya Haruna, ya bayyana gamsuwa da wannan yarjejeniya da kasar China bisa wasu dalilai. Ku latsa alamaru sauti don sauraren cikakkiyar hirar.

  • Dr Rakiya Sa’idu kan halin da ƴan Najeriya da ke Afirka ta Kudu ke ciki

    05/05/2026 Duration: 03min

    Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa za ta fara kwashe ƴan ƙasarta da ke son komawa gida daga Afirka ta Kudu, matakin da ta ce ya zama dole saboda tsananin kyamar baƙi da kuma rahoton mutuwar wasu ƴan Najeriya biyu sakamakon hare-haren da ake kai wa ƴan cirani. Akalla 'yan Najeriya 130 ne suka riga suka yi rajista don neman a kwashe su zuwa gida, sakamakon fargabar makomarsu na rashin tabbas. Dakta Rakiya Sa’idu daga jami’ar Capetown, ta bayyana mana yadda ƴan siyasa ke amfani da lokacin zaɓe wajen rura wutar wannan matsala. Ku latsa alamar sauti don jin tattaunawar da Shamsiyya Haruna ta yi da ita............

  • Alhaji Muhammed Sani Zoro tsohon shugaban NUJ kan ranar ƴan jarida ta duniya

    04/05/2026 Duration: 03min

    Kamar dai kowace shekara, 3 ga watan Mayu ita ce ranar kare ƴancin aikin yaɗa labarai a duniya, inda rahotannin da ƙungiyoyin da ke fafutuka a wannan fage ke nuni da cewa an samu gagarumin koma-baya ta fannin aikin jarida a cikin shekarar da ta gabata. Dangane da wannan rana, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da tsohon shugaban ƙungiyar Ƴan Jarida ta Najeriya (NUJ) Honnorable Alhaji Muhammed Sani Zoro, wanda da farko ya fara yin tsokaci a game da irin sauye-sauyen da aka samu a aikin jarida saboda dalilai masu nasaba da zamani. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.

  • Tinubu ya ce babu gudu ba ja da baya kan samar da ƴan sandan jihohi

    01/05/2026 Duration: 03min

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada aniyar sa ta samar da Yan Sandan jihohi domin samar da tsaro. Tinubu ya bayyana haka ne yayin ganawa da masu ruwa da tsaki na jihar Filato mai fama da tashin hankalin. Alhaji Isa Tafida Mafindi, wanda ya wallafa littafi a kan samar da Yan Sandan jihohi ya mana tsokaci a kai, yayin tattaunawar su da Bashir Ibrahim Idris. Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...

  • Fargaba ta mamaye zukatan ƴan Najeriya dangane da makomar adawa a ƙasar

    30/04/2026 Duration: 03min

    Yan Najeriya na cigaba da bayyana fargaba dangane da makomar ƴan adawar ƙasar dangane da zabe mai zuwa , la'akari da cewar akasarin jami'iyyun adawar na fama da rikice-rikicen da ka iya hana su takara. Akan wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Alhaji Kabir Muhammad Baba, ɗan siyasa a jihar Bauchi. Shiga alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar......

  • Dakta Kabiru Inuwa Dukawa kan yadda ƙin jinin baƙi a Afrika ta Kudu ke ƙaruwa

    29/04/2026 Duration: 03min

    Ɗaruruwan ‘yan Afrika ta Kudu masu ƙyamar baƙi, sun gudanar da zanga-zanga jiya Talata a birnin Pretoria, bayan da suka bjirewa kiran da shugaban ƙasar Cyril Ramaphosa ya yi musu na dakatar da kai wa baƙi hare-hare gami da cin zarafinsu, inda a baya bayan wasu ‘yan Najeriya biyu suka rasa rayukansu. Cin zarafin baƙin da tsagerun ‘yan Afrika ta Kudun na baya bayan nan dai ya fara ne da shafar ‘yan ƙasashen Ghana, da Habasha da Zimbabwe kafin kai wa ga ‘yan Najeriya. Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Kabiru Inuwa Dukawa, masanin siyasar ƙasa da ƙasa da ke Najeriya. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakkiyar Hirar.

page 1 from 2