Bakonmu A Yau

Dakta Kabiru Inuwa Dukawa kan yadda ƙin jinin baƙi a Afrika ta Kudu ke ƙaruwa

Informações:

Synopsis

Ɗaruruwan ‘yan Afrika ta Kudu masu ƙyamar baƙi, sun gudanar da zanga-zanga jiya Talata a birnin Pretoria, bayan da suka bjirewa kiran da shugaban ƙasar Cyril Ramaphosa ya yi musu na dakatar da kai wa baƙi hare-hare gami da cin zarafinsu, inda a baya bayan wasu ‘yan Najeriya biyu suka rasa rayukansu. Cin zarafin baƙin da tsagerun ‘yan Afrika ta Kudun na baya bayan nan dai ya fara ne da shafar ‘yan ƙasashen Ghana, da Habasha da Zimbabwe kafin kai wa ga ‘yan Najeriya. Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Kabiru Inuwa Dukawa, masanin siyasar ƙasa da ƙasa da ke Najeriya. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakkiyar Hirar.