Bakonmu A Yau
Hajiya Fatsuma Adamu shugabar makarantar da Boko Haram ta sace ɗalibai a Askira-Uba
- Author: Vários
- Narrator: Vários
- Publisher: Podcast
- Duration: 0:03:22
- More information
Informações:
Synopsis
Gwamnan jahar Borno Babagana Umara Zullum ya ce, gwamnati da jami’an tsaro na ƙoƙarin ceto daliban makaranta da aka sace a makarantar firamare a ƙauyen Mussa dake ƙaramar Hukumar Askira- Uba. Gwamna Zulum ya bayyana haka ne ya yin wata ziyarar jaje da ya kai Askira Uba dangane da iftila’in da ake dangantawa da Boko Haram. Ziyarar na zuwa ne yayin da aka shiga kwanaki na 5 da sace daliban ciki harda kanan yara. Shugabar kula da ilimi na ƙaramar Hukumar Askira-Uba, Hajiya Fatsuma Adamu Askira ta bayyana mana halin da ake ciki, a tattaunawarta da Ahmad Abba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.