Synopsis
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episodes
-
Dakta Muhammad Garba kan matsanancin halin yunwa da ake ciki a Najeriya
28/04/2026 Duration: 03minWani rahoton masana na hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya da aka fitar a ƙarshen makon jiya, ya sanya Najeriya a cikin jerin ƙasashe 10 da suka fi fama da Yunwa a Duniya. A Najeriya rahoton ya ƙiyasta zuwa wannan shekara, aƙalla mutane miliyan 35 ke fuskantar haɗarin faɗawa cikin ƙangin Yunwa, saboda ƙarancin abincin da ake fama da shi a sassa da dama, musamman a yankunan karkara na arewacin ƙasar inda mafi rinjayen manoma suke. Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Muhd Garba, malami a tsangayar koyar da Ilimin ayyukan Noma a Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke garin Bauchi. Ku danna alamar saurare domin jin cikakkiyar tattaunawar tare da Nura Ado Sulaiman.
-
Soumaila Amadou akan harin ta'addancin Mali da ya kashe ministan tsaro
27/04/2026 Duration: 03minAn shiga zaman zullumi a Mali bayan da ƙawancen ƙungiyar Abzinawa ƴan tawaye FLA da kuma kungiyoyin da ke ikirarin jihadi suka ƙaddamar da farmaki kan birane da dama na ƙasar tun a ranar asabar har zuwa jiya lahadi. Tuni dai aka tabbatar da mutuwar ministan tsaro Janar Sadio Camara da kuma wasu mutane da dama a wannan farmaki da ake kallo a matsayin mafi tsaruwa da kuma jajircewa daga waɗannan ƙungiyoyi da suka share tsawon shekaru suna fafatawa da dakarun gwamnati. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Malam Soumaila Amadou, mai sharhi kan lamurran yankin Sahel, ga kuma zantawarsu. Latsa alamar sauti don sauraron hirar Abdoulkarim Ibrahim da Soumala Amadou:
-
Gwamnonin Najeriya 20 sun amince da gina katafariyar rugar zamani
24/04/2026 Duration: 03minKimanin gwamnonin jihohin Najeriya 20 sun amince su gina katafariyar ruga ta zamani a jihohinsu wadda za ta kunshi makarantu da asibitoci da kasuwanni har ma da wuraren kiwon dabbobi musamman shanu da zummar zaunar da Fulani makiyaya wuri guda ba tare da gararanba ba. Tuni masana suka ce wannan sabon tsarin zai yi tasiri wajen tabbatar da lafiyar dabbobin Najeriya tare da ruɓanya adadin madarar da suke samarwa a kullum. Jim kaɗan da kammala taro kan wannan shiri a birnin Lagos, Abdurrahman Gambo ya tattauna da Farfesa Abba Gambo, mai bai wa gwamnonin Najeriya shawara kan noma da kiwo. Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...
-
Dakta Harbau akan yawan iskar gas da Najeriya ta fitar
23/04/2026 Duration: 03minWasu alƙaluma daga Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur na kan tudu da na cikin ruwa (NMDPRA) sun nuna cewa, adadin Iskar Gas ɗin da aka fitar daga Najeriya zuwa kasuwannin ƙetare ya kai kaso 62 cikin 100, cikin watanni uku na farkon wannan shekara. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Gas ɗin ya yi ƙaranci a Najeriyar, lamarin da ke taka rawa wajen raguwar hasken lantarkin da ake samu, fannin da kasonsa aƙalla 80 cikin 100 ya dogara da arziƙin na Gas. Don jin yadda masana ke kallon lamarin da kuma mafita, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Aminu Idris Harbau, ƙwararren kan tattalin arziki a Najeriya. Latsa alamar sauti don sauraron hirar: