Ilimi Hasken Rayuwa

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 3:59:57
  • More information

Informações:

Synopsis

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da fasaha da ke naman saukakawa Danadam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Biladam. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe.

Episodes

  • Ɗimbin matasa na haƙura da karatun boko saboda rashin tabbas kan samun aiki

    19/05/2026 Duration: 10min

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda matasa a baya-bayan na ke haƙura da ilimin boko saboda shakku kan yiwuwar samun aikin yi. Matsalar rashin aikin yi bayan shafe tsawon shekaru ana karatu tare da kashe maƙuden kuɗaɗe ya sanya matasa da dama musamman waɗanda ba ƴaƴan wasu ba ajje tunanin karatu tare da mayar da hankali a kasuwanci da koyon sana'a saboda abin da suka kira rashin tabbas na cin moriyar karatun da suka yi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • An yafe wa ɗaliban da ke son shiga kwalejin ilimi rubuta JAMB a Najeriya

    12/05/2026 Duration: 09min

    A yau muna ɗauke da wani labari mai daɗi ga ɗaliban da ke sha’awar zama malamai da kuma masu son shiga Kwalejin Ilimi a faɗin Najeriya. Gwamnatin ta fitar da wasu sabbin tsare-tsare da nufin sauƙaƙa wa ɗalibai hanyar neman ilimi da kuma ƙarfafa musu gwiwa ta fuskar kuɗi. Ministan Ilimi Tunji Alausa, ya sanar da cewa ɗaliban da ke son shiga Kwalejin Ilimi yanzu ba sai sun rubuta jarrabawar UTME ba. Amma dole ne ɗalibi ya kasance yana da aƙalla darussa biyar a sakamakonsa na sakandare. Duk da cewa ɗalibi ba zai rubuta jarrabawa ba, dole ne ya yi rajista da hukumar JAMB don tantance takardunsa domin samun gurbin karatu ta tsarin CAPS. Bayan rage wa ɗalibai wahalar jarrabawa, gwamnatin ta kuma samar da tallafin karatu domin jawo hankalin kwararru zuwa fannin koyarwa. inda ta amince da biyan ɗaliban da ke karatu a kwalejojin ilimi na gwamnati alawus din naira naira 50,000 a kowane zango, waɗanda ke karatun digiri a fannin ilimi a jami’o’in gwamnati za su samu naira naira 75,000 Masana a fannin ilimi dai na ganin c

  • Tasirin fasahar zamani wajen bunƙasuwar aikin jarida

    05/05/2026 Duration: 09min

    Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan bikin ranar ƴancin ƴan Jaridu ta duniya da ke gudana a kowacce ranar 3 ga watan Mayu, bikin da ke zuwa a wannan karon cikin wani yanayi da aikin na Jarida ke ganin koma baya. Akwai dai ƙorafe-ƙorafe daga sassa daban-daban kan yadda aikin  na Jarida ke fuskantar barazana kodayake masu ruwa da tsaki a wannan fanni sun ce yanayin yaɗa labaran ya samu ci gaba da matuƙa ta sakamakon yaɗuwar fasahar zamani. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Yadda makarantun tsangaya suka fara gauraya karatun addini da na Boko don tafiya da zamani

    28/04/2026 Duration: 09min

    Shirin Ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda makarantun tsangaya da na Islamiyya suka fara gauraya karatun addini da na zamani a ƙoƙarin da suke yi na tafiya da zamani da kuma amun tallafi daga gwamnatoci da manyan ƙungiyoyi na duniya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

  • Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu - kashi na 2

    22/04/2026 Duration: 10min

    Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon ci gaba ne kan yadda wasu daga cikin iyaye mata ke fafutukar neman ilimi a Kano, duba da yadda a wasu makarantu ake tambayar matakin karatunsu kafin ɗaukar yaran su a matsayin ɗalibai. Mafi yawan iyaye lamarin baya musu daɗi, wasu na zargin ƙin ɗaukar yaran, sai dai hanzarin shine sanin irin kulawar da ya kamata makarantun su baiwa yaran ne yasa suke tambayar. Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna..............

  • Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu - kashi na 2

    21/04/2026 Duration: 10min

    Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon ci gaba ne kan yadda wasu daga cikin iyaye mata ke fafutukar neman ilimi a Kano, duba da yadda a wasu makarantu ake tambayar matakin karatunsu kafin ɗaukar yaran su a matsayin ɗalibai. Mafi yawan iyaye lamarin baya musu daɗi, wasu na zargin ƙin ɗaukar yaran, sai dai hanzarin shine sanin irin kulawar da ya kamata makarantun su baiwa yaran ne yasa suke tambayar. Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna..............

  • Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu

    14/04/2026 Duration: 10min

    A arewacin Najeriya, shigar mata makarantun yaki da jahilci ya fara ne a matsayin wani yunkuri na inganta rayuwar iyali da kuma tarbiyyar yara, inda mata da dama sun fahimci cewa rashin ilimi na hana su taimaka wa yaransu wajen karatunsu na zamani da kuma kulawa da lafiyarsu. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

  • Yadda wani matasa ya ƙirƙiri jirgi marar matuƙi a jihar Kano da ke Najeriya

    07/04/2026 Duration: 10min

    Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon, ya yi dubi ne kan yadda wani matashi a jihar Kanon Najeriya ya ja hankalin jama’a, bayan ƙirƙirar jirgi maras matuƙi, daidai lokacin da matasan wannan ƙasa ke faɗi tashin yadda za su samo masu ɗaukar nauyin ayyukan fasahar da suke son cimmawa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruwa...........

  • Yadda wasannin na'ura kwamfita ke samun karɓuwa a tsakanin matasa

    31/03/2026 Duration: 09min

    Shirimmu na ilimi hasken rayuwa na wannan mako yayi karin bayani akan wasannin na’ura kwamfuta  masu kama da gaske da aka fi sani da virtual reality a turance. Danna alamar sauti domin sauraron karin bayani........

  • Tasirin faɗowar wasu sinadarai daga sama a fagen kimiyya da fasaha

    03/03/2026 Duration: 09min

    Shirin "Ilimi Hasken Rayuwa" na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya yada zango ne a Jamhuriyar Nijar inda abaya-bayan nan aka rika samun fadowar wasu abubuwa daga sararin samaniya, lamarin da ke ci gaba da faruwa a sassan a kasar. A baya bayan ne dai wasu abubuwa suka fado daga sararin samaniya a kauyuka 5 daban daban a yankin Kornaka, da Dakwaro da suka hada da Dan Madi, Baushi, da sauransu, haka abin ya taba kasancewa a 2021 inda aka samu wani babban dutse da ya fado daga sama a garin Aikawa na yankin Gazawa sannan, an samu wasu duwatsun a yankin Tanut, Agades da sauran yankunan Nijar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...

  • Ra'ayoyi sun banbanta kan amfani da fasahar AI wajen yin tiyata

    24/02/2026 Duration: 10min

    Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako a wannan makon, ya mayar da hankali kan binciken da ya gano cewa shigar fasahar AI cikin fannin tiyata na haifar da wasu matsaloli masu kama da barazana ga rayuwar ɗan adam, kan haka ne ma muka zanta da masana a fannin kimiyya da kuma ɓangaren lafiya, inda muka jiyo ra’ayoyin mutane game da yadda wasu ke yarda AI ya duba lafiyarsu har ta kai ga tiyata a wasu lokutan. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna............

  • Yadda satar jarabawa ke taka rawa wajen kassara ingancin ilimi a Najeriya

    17/02/2026 Duration: 10min

    Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda satar jarabawa ke ƙoƙarin zama ruwan dare a makarantun sassan Najeriya, matsalar da ke ci gaba da illa ga ingancin ilimi a dukkan makarantu na ƙasar. Akwai zarge-zargen da ke nuna cewa wasu daga cikin jami'an hukumomin da ke kula da shirya jarabawa a matakai daban-daban na taimakawa wannan mummunar ɗabi'a ta satar jarabawa ta hanyar fallasa amsoshin tambayoyin da ake shirin fitarwa ga ɗalibai. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Yadda masu larurar ji ke fama da ƙalubalen karatu a Najeriya

    10/02/2026 Duration: 09min

    Shirin na wannan mako ya ba da hankali ne akan yadda masu fama da larurar ji ke fama da ƙalubalen karatu a wasu sassan Najeriya.

  • Ana fuskantar koma bayan koyan harshen larabci a arewacin Najeriya

    03/02/2026 Duration: 09min

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali ne kan dalilan da suka haddasa rashin koyon ingantaccen larabci tsakanin daliban sakandare a arewacin Najeriya, sabanin lokutan baya. A shekarun baya, alkaluma sun nuna cewa kusan kaso hamsin na larabcin da Dalibai ke koya suna samun sa ne a makarantun boko ba lallai sun sun halarci makarantun Arabiya, al’amarin dake neman zama tarihi a wannan zamani. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......

  • Yadda satar jarabawa da cin hanci da rashawa ke kassara ɓangaren Ilimi a Kamaru

    27/01/2026 Duration: 09min

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda wani bincike can a Jamhuriyyar Kamaru ya gano yadda satar Jarabawa da cin hanci da rashawa ke mummunan tasiri a ɓangare ilimin ƙasar. Matsalar ta cin hanci da rashawa kai tsaye ta yi mummunar illa ga yanayin ɗaukar malamai aiki da gina makarantu ko kuma samar da ci gaba a ɓangaren na Ilimi, yayinda a gefe guda satar jarabawar da ɗalibai ke yi ke zagon ƙasa ga makomar ilimi a ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Makomar karatu a yankin arewacin Najeriya cike da barazanar ƴanbindiga

    20/01/2026 Duration: 09min

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali kan makomar karatun ɗalibai a makarantun Najeriya musamman yankin arewaci mai fama da matsalolin tsaro, dai dai lokacin da aka koma sabon zangon karatu Iyaye na cike da fargaba kan tsaro a makarantu. Makwanni gabanin tafiya hutun zangon da ya gabata cikin watan Nuwamban bara ne, hare-haren ƴan bindiga suka tilasta kulle makarantu a sassan arewacin Najeriyar ciki har da makarantun Unity da ke ƙarƙashin kulawar gwamnatin Tarayya. Wasu na da ra'ayin cewa sai an haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin dukkanin ɓangarori ne, ɗalibai za su samu cikakken tsaro a makarantu tare da samun ɗorewar Ilimi a yankin. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

  • Kashi na biyu kan yadda sabuwar manhajar fassarawa da lissafa haraji ke amfani a Najeriya

    06/01/2026 Duration: 09min

    A kashi biyu na shirin ilimi hasken rayuwa, mun ɗora kan sabuwar manhajar fassarawa da da sauƙaƙa lissafin karɓar haraji. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Faruk Yabo.

  • Farfesa Aminu Bello ya samar da manhaja mai sauƙaƙa lissafin haraji a Najeriya

    30/12/2025 Duration: 09min

    Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya tattauna da Farfesa Aminu Bello Usman daga  Birtaniya, ɗan jihar Kano da ke tarayyar Najeriya, wanda ya ƙirƙiri wata Manhaja da za ta taimaka wa mutane wajen sauƙaƙa musu lisaffin hada-hadar kuɗaɗe musamman ma na haraji. Wani abin ban sha’awa dangane da Manhajar da aka fi sani da Software a Turance, shi ne yadda wannan manhajar ta ƙunshi harsuna biyar. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nasir Sani.

  • Akwai bukatar samarwa masu buƙata ta musamman ayyukan yi domin dogaro da kai

    23/12/2025 Duration: 09min

    Mutane da suka tsinci kansu a cikin masu buƙata ta musamman sakamakon nau’ikan nakasar da suka fama da ita sun share shekaru suna fuskantar giɓi babba a muhimman fannonin rayuwa daban daban, ciki kuwa har da samun guraben ayyukan yi ko da kuwa a ce sun yi katarin tsallake shingen samun ilimi, matsalar da ta fi ƙamari a ƙasashe masu tasowa ciki har da na Nahiyar Afrika. Mutane da suka tsinci kansu a cikin masu buƙata ta musamman sakamakon nau’ikan nakasar da suka fama da ita sun share shekaru suna fuskantar giɓi babba a muhimman fannonin rayuwa daban daban, ciki kuwa har da samun guraben ayyukan yi ko da kuwa a ce sun yi katarin tsallake shingen samun ilimi, matsalar da ta fi ƙamari a ƙasashe masu tasowa ciki har da na Nahiyar Afrika. Kan wannan batu shirin Ilimi Hasken rayuwa na wannan lokaci zai tattauna, bayan da ya yi tattaki zuwa Jihar Jigawa da ke tarayyar Najeriya, akan ƙorafin da wasu fama da nakasar suka yi a bisa ganin cewar suna neman rasa damar samun guraben ayyukan yi da suka cancanci dafewa.   A

  • Makarantu a Kano sun fara kai ƙarar iyayen yara sabida bashin kuɗin makaranta

    09/12/2025 Duration: 09min

    Shirin ilimi Hasken rayuwa na wannan mako dubi ne kan yadda makarantu masu zaman kan a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, suka fara ɗaukar matakin kai ƙarar iyayen yara gaban hukumomi, sakamakon rashin biyansu kuɗaɗen karatun ƴaƴansu na tsawon lokaci. Abin damuwar shine, idan iyayen suka tara kuɗin makaranta har ya kai matakin da ba za su iya biya ba, sai su sauya wa yaran nasu wurin makarantu, kenan wancan kuɗi da ake binsu ya bi ruwa. Babbar matsalar ita ce, wannan al’amari a wasu lokutan ya kan haifar da ƙalubale ga ɓangarorin da ke gudanar da irin wadannan makarantu, abin da har ke kaiwa ga rufewa ko kuma sayar da makaranta, saboda rashin isassun kuɗin da za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna..........

page 1 from 2