Ilimi Hasken Rayuwa

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 3:59:57
  • More information

Informações:

Synopsis

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da fasaha da ke naman saukakawa Danadam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Biladam. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe.

Episodes

  • Rashin albashi na shafar aikin koyarwa a makarantu masu zaman kansu a Najeriya - Rahoto

    02/12/2025 Duration: 10min

    A wannan makon, shirin yayi dubi ne kan batun yadda har kawo yanzu ake samun malaman makaratu masu zaman kansu a Najeriya dake ɗaukar albashin Naira dubu 15 zuwa sama, maimakon mafi ƙaranci albashin naira dubu 70 da gwamnati ƙasar ta yi dokar biya. Duk da irin kuɗaden da ake shatawa iyayen yara, har ta kai idan yaronka ba a biya mishi kuɗin makaranta ba, to kuwa za a kora maka shi gida, hakan be sanya sun inganta albashin malaman ba. Makaranta mai zaman kanta mutum ke kafa ta ko haɗin gwiwa na wasu mutane domin taimakawa ko ba gudunmawa yayin da a wannan lokaci da dama sun mayar da ita matsayin kasuwanci, abin da masana ke ganin kenan akwai buƙatar Malamai su samu yanayi mai kyau da walwala wanda ta hakanne zasu samu ƙwarin gwiwa wajan bayar da ilimi mai nagarta. Hauwa'u Adam dake koyarwa a wata Makarata dake yankin Jambulo a jihar Kanon Najeriya, ta sheda mana cewa saboda karatunta yakai matakin digiri ne ake biyanta Naira dubu 20, amma masu kwalin babbar difloma ta HND da NCE albashin daga dubu 17 ne zuwa 1

  • Makomar ilimi dalilin rufe makarantu sabida matsalar tsaro a Najeriya

    25/11/2025 Duration: 10min

    A wannan makon shirin ya karkata akala ne kan makomar ilimi a Najeriya, inda hukumomi suka fara rufe makarantu saboda matsalolin tsaro da ke neman dakushe makomar ilimin manyan gobe. Me yasa jihohi ke gaggawar rufe makarantu bayan sace ɗalibai a Kebbi da Niger a kwanan nan? Shin babu wasu hanyoyin kawo ƙarshen matsalar tsaro sai dai rufe makarantu?   Tambayar kenan da ‘yan Najeriya ke yiwa gwamnatin ƙasar, yayin da ake ganin tarin jami’an tsaro na yiwa masu rike da manyan makamai rakiya, abin da ke nuna yawan jami’an tsaron da ƙasar ke da shi idan aka haɗa ƴansanda da sojoji da jami’an tsaron Civil Defence da sauransu, to kuwa iyaye suka ce idan har aka yi la’akari da wannan za a iya samarwa ɗalibai tsaro. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.........

  • Har yanzu Malama tsangaya na amfani da Ajami wajen musayar sakonni

    11/11/2025 Duration: 09min

    Shirin a wannan mako, kareshe ne kan maudu’in da muka tattaunawa a makonni biyun da suka gabata, wanda ya mayar da hankali kan yadda rubutun Ajami a kasar Hausa ya yi shura, da kuma yadda yake neman bacewa a wannan zamani. Yayin da ake ganin har yanzu a Jamhuriyar Nijar, akwai yankunan da suke amfani da ajami wajen isar da sakonni, Malaman tsangaya daga Najeriya ma suna amfani da wannan tsarin rubutu wajen musayar bayanai a tsakaninsu. Yaɗuwar addinin Islama a Ƙasar Hausa masana suka ce, ya taimaka sosai wajen shaharar wannan salo na rubutu, sannan kuma ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen inganta hanyoyin sadarwa na wancan lokaci. A tattaunawarmu da masanin tarihi daga Kanon Najeriya, farfesa Tijjani Naniya, ya bayyana cewa, zuwan turawan mulkin mallaka, shine musabbabin gushewar wannan rubutu a kasar Hausa, amma a wancan lokaci, rubutun na ajami ya ci kasuwa tsakanin masana, malamai, sarakuna da kuma ‘yan kasuwa.

  • Tasirin rubutun Ajami wajen musayar bayanai tsakanin al'ummar Hausawa ( 2)

    04/11/2025 Duration: 10min

    Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya cigaba ne da mayar da hankali kan makomar rubutun Ajami a ƙasar Hausa, nau'in rubutun da ya taimaka matuƙa wajen musayar bayanai tsakanin al'ummar Hausawa tun gabanin zuwan Turawan mulkin mallaka.     A shekarun baya-bayan nan rubutun na Ajami ya zama tarihi a ƙasar Hausa bayan da kowanne ɓangare ya rungumi tsarin boko daga turawan Yamma. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin kashi na biyu:

page 2 from 2