Bakonmu A Yau

Soumaila Amadou akan harin ta'addancin Mali da ya kashe ministan tsaro

Informações:

Synopsis

An shiga zaman zullumi a Mali bayan da ƙawancen ƙungiyar Abzinawa ƴan tawaye FLA da kuma kungiyoyin da ke ikirarin jihadi suka ƙaddamar da farmaki kan birane da dama na ƙasar tun a ranar asabar har zuwa jiya lahadi. Tuni dai aka tabbatar da mutuwar ministan tsaro Janar Sadio Camara da kuma wasu mutane da dama a wannan farmaki da ake kallo a matsayin mafi tsaruwa da kuma jajircewa daga waɗannan ƙungiyoyi da suka share tsawon shekaru suna fafatawa da dakarun gwamnati. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Malam Soumaila Amadou, mai sharhi kan lamurran yankin Sahel, ga kuma zantawarsu. Latsa alamar sauti don sauraron hirar Abdoulkarim Ibrahim da Soumala Amadou: