Bakonmu A Yau

Dakta Muhammad Garba kan matsanancin halin yunwa da ake ciki a Najeriya

Informações:

Synopsis

Wani rahoton masana na hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya da aka fitar a ƙarshen makon jiya, ya sanya Najeriya a cikin jerin ƙasashe 10 da suka fi fama da Yunwa a Duniya.  A Najeriya rahoton ya ƙiyasta zuwa wannan shekara, aƙalla mutane miliyan 35 ke fuskantar haɗarin faɗawa cikin ƙangin Yunwa, saboda ƙarancin abincin da ake fama da shi a sassa da dama, musamman a yankunan karkara na arewacin ƙasar inda mafi rinjayen manoma suke. Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Muhd Garba, malami a tsangayar koyar da Ilimin ayyukan Noma a Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke garin Bauchi. Ku danna alamar saurare domin jin cikakkiyar tattaunawar tare da Nura Ado Sulaiman.