Kasuwanci

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 4:11:52
  • More information

Informações:

Synopsis

Shirin yakan diba kasuwancida tattalin arizikin kasashen duniya ya ke ciki. Shirin yakan ji sabbin dubaru da hajojin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masanaantu dangane da halin da suke ciki.

Episodes

  • Koken ƴan Najeriya kan yadda bankuna ke zare musu kuɗi daga asusun ajiyarsu

    20/05/2026 Duration: 10min

    Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan yadda ƴan Najeriya, ke nuna fushinsu dangane da zargin cire musu kuɗi ba bisa ka’ida ba daga asusun bankunansu. Miliyoyin 'yan Najeriya da yanzu haka ke fuskantar hauhawan farashin kayayyaki da kuɗin sufuri, da kuma rashin tabbas ga makomarsu a fannin tattalin arziki, caje-caje da dama da bankuna ke yi a asusun ajiyarsu na sake jifasu cikin damuwa. A cikin 'yan watannin nan, koke-koke sun mamaye kafofin sada zumunta, sakamakon rashin karin bayani kan yawaitan kudaden da bankunan ke cirewa.. Duk da cewa bankuna sun dage cewa hakan tsari ne da kuma sahalewar haka daga babban bankin kasar CBN, kwastomi na diga ayar tambaya kan cirewa  fiye sau ɗaya kan, ko kuma daga wanda ya tura da kuma wanda ya ƙarba, yayin da wasu ke kokawa kan rashin maida musu kudinsu nan take idan aka samu masalar sabis kudi bai je ga wanda aka tura ba da dai sauransu... Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Yadda ƴan kasuwa a Najeriya suka jingine harakokinsu saboda tsadar sufuri

    13/05/2026 Duration: 10min

    Shirin Kasuwa akai miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu . Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......

  • Yadda tsadar sufuri ya tilastawa 'yan kasuwa jingine sana'o'insu a Najeriya

    13/05/2026 Duration: 10min

    A yau shirin ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu . Sannu a hankali, irin hada-hadar da aka saba gani tsakanin mafi yawan kasuwannin Nigeria na neman zama abun tarihi, sakamakon yadda ‘yan kasuwa masu tarin yawa suka jingine harkokinsu na kasuwanci saboda tsadar sufuri. ‘Yan kasuwa, na kukan samun wagegen gibi tsakanin uwar kudin jarinsu da abinda suke kashewa na safarar kayansu zuwa kasuwanni, saboda tsadar kudin sufuri da kuma rashin ciniki saboda halin rashin kudi da ‘yan kasar ke ciki. Kasancewar kowane sasshen Nigeria na da nau’in kayayyakin da yake da su a wadace, ‘yan kasuwa daga arewacin kasar, kan saro kayayyaki irin su Manja da Man Gyada da Garin Kwaki da makamantan su, daga kudancin kasar, yayinda ‘yan kasuwa daga kudanci, kan sayi hatsi, dabbobi da makamantan su daga arewacin kasar. Bayanan hukumar kididdiga ta Nigeria, sun yi nuni da cewa damar ikon sayen kay

  • Damarmaki da kuma ƙalubalen da manoman Albasa a arewacin Kamaru ke fuskanta

    29/04/2026 Duration: 09min

    Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon, ya duba  ƙalubale da kuma damammaki a ɓangaren noman albasa a arewacin Kamaru. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

  • Matakan da bankin CBN ke ɗauka na sake fasalin tsarin harkokin kuɗi a Najeriya

    22/04/2026 Duration: 10min

    Shirin Kasuwa akai miki doke na wannan mako ya yi duba ne kan matakan da babban bankin Najeriya CBN ke ɗauka na sake fasalin tsarin harkokin kuɗaɗe, domin rage hauhawan farashin kayayyaki a kasuwanni da kuma daga darajar kuɗin ƙasar wato Naira, ta hanyar rage kuɗaɗe da ke yawo a hannun jama’a. Babban Bankin Nigeria, ya fito da bakin alƙalamin adadin kuɗaɗen da ke bankuna da waɗanda ake hada-hada da su a cikin ƙasa tare da waɗanda jama’a ke jujjuyawa a hannunsu. Adadin wannan kudi dai a cewar bankin na CBN, ya kai Naira Triliyan 123 da biliyan 15, a watan Fabareiru, inda aka samu raguwar adadin madarar kuɗi da ke hannun jama’a akan na watan Janairu, wanda ya kai Nera Triliyan 123 da biliyan 36. Haka ma adadin kudaden kasar a asusun ajiyarta na ketare ya ragu zuwa Nera Triliyan 28 da biliyan 41 daga Nera biliyan 29 da biliyan 61. Ku latsa alamar sauti don sauti don sauraron cikkan shirin tare da Ahmad Abba.............

  • Yadda matsalolin tsaro ke kassara kasuwanci a arewacin Najeriya

    08/04/2026 Duration: 10min

    Shirin na wannan makon ya mayar da hankali ne kan irin fargabar da 'yan kasuwar arewacin Najeriya da ke fatauncin kayayyaki zuwa wasu sassan jihohi ke ciki, sakamakon ayyukan bata gari da ke tare hanya wanda a wasu lokuta kan kai ga rasa rayuka. Abune da aka saba gani, ‘yan kasuwar dake hada Hada tsakankin jihohi daga wannan kasuwa zuwa waccan ko tsakanin kasuwannin kauyuka. To sai dai Kuma irin wannan tsarin na fuskantar cikas ko koma baya, alal misali ga yan kasuwa a jihar filato dake arewacin Najeriya, sakamakon munanan halaye na wasu bata gari marasa tausayin rayuwar Dan Adam, dake tare Yan tireda ko Kuma matafiya inda suke Kai musu farmaki, tare da yi musu kisan gilla. A kwanakin baya wasu Bata gari sun tare wasu Yan kasuwa da ke fatauci daga garin Jos zuwa yankin kudancin Jihar, inda suka kashe biyar daga cikinsu, Wannan  al’amari ya Sanya Yan Kasuwar da sauran matafiya shiga hali na fargaba a kowane yanki dake jihar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Yadda matasa ke fatan cin gajiyar yarjejeniyar tattalin arziki tsakanin Nijar da Algeria

    01/04/2026 Duration: 09min

    Matasa a Agadez da ke arewacin Jamhuriyar Nijar na cike da fatan cin moriyar sabuwar dangatakar da aka kyautata tsakanin kasar da makwabciyarsu Aljeriya. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

  • Koma bayan da kasuwancin duniya ya fuskanta sakamakon rikicin Gabas Ta Tsakiya

    18/03/2026 Duration: 10min

    Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" tare da Ahmed Abba a wannan mako ya ɗora ne kan inda ya tsaya a makon jiya, game da gagarumin koma baya a fannin kasuwanci da tattalin arziki da duniya ke fuskanta masamman a bangaren makamashi, sakamakon yaƙin da kawancen Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran, da kuma martinin jamhuriyar musuluncin kan Isra’ila da muradun Amurka a kasashen labarawa suka janyo. A makon jiya, shirin ya tattauna wannan batu ne da malaman da muka gayyato, wato Dr. Aminu Idris Harbau masamanin tattalin arziki a tarayyar Najeriya, da Dr. Ibrahim Adamu na sashin nazarin yankin gabas ta Tsakiya a jami’ar Havard da ke Dubai na haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, sai Mohammad Qaddam Sidiq Isa, mai sharhi kan al’amuran Yau da Kullum shima a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, sai kuma Isma’il Albabawee ɗan jarida kuma ɗalibi a jami’ar Karbala a ƙasar Iraki. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Yadda yaƙin Iran ya haifar da koma baya ga tattalin arzikin Duniya

    11/03/2026 Duration: 09min

    A yau shirin Kasuwa A kai Miki Dole na wanan mako tare da Ahmad Abba ya mayar da hankali ne a kan yadda Yaƙin da kawancen Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran, da hare-haren mayar da martini na jamhuriyar musuluncin kan yahudun Isra’ila da muradun Amurka a kasashen labarawa suka janyo gagarumar koma baya a fannin kasuwanci da tattalin arzikin duniya masamman a bangaren makamashi.     Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin......

  • Yadda aka gudanar da taron tattalin arzikin a Akwa Ibom

    04/03/2026 Duration: 09min

    Shirin Kasuwa A kai Miki Dole na wanan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan taron taron tattalin arziki da ya gudana a farkon watan Fabarairun da ya gabata a jihar Akwa Ibom da ke kudancin Najeriya. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....

  • Najeriya da China sun yi bukin cika shekaru 55 da hulɗar diflomasiyya

    18/02/2026 Duration: 17min

    Shirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan tasirin tattalin arziki dangane da alaƙar China da Najeriya da a makon jiya aka yi bikin cika shekaru 55 da faro hulɗar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu. Najeriya da China sun sake jaddada karfafa dangantakar diflomasiyya da ke tsakaninsu yayin da kasashen biyu ke bikin cika shekaru 55 da fara huldar diflomasiyya a bikin baje kolin sabuwar shekarar kalandar kasar China da aka gudanar.

  • Yadda buɗe iyakokin Najeriya da Nijar zai taimaka wajen haɓaka kasuwanci

    11/02/2026 Duration: 10min

    Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan wani sabon yunkuri na kara inganta alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da Nijar inda hukumar kwastom a jamhuriyar Nijar tayi tattaki zuwa Najeriya don tattaunawa hanyoyin da za’a bi don saukaka hada-hadar kayayyaki tsakanin kasashen biyu. Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam na Najeriya Adewale Adeniyi, ya sake jaddada aniyar Hukumar na sauƙaƙe cinikayya a yankin, ta hanyar saukaka jigilar kayayyaki da kuma haɓaka haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen da ke makwabtaka da su, musamman Jamhuriyar Nijar. Adeniyi ya bayyana hakan ne a ranar Juma'ar da ta gabata,  yayin wani babban taron haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Kwastam ta Najeriya da takwararta ta Jamhuriyar Nijar, ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar, Muhammadu Yaqouba, da aka gudanar da hedikwatan  Kwastam da ke Maitama a Abuja. Tawagar Nijar ta kunshi shugabannin cibiyar inganta kasuwanci na Nijar wato Chamber des Commerce. Cikin mahimman abubuwan da aka duba a ganawar akwai saukaka

  • Yadda gwamnatin jihar Yobe ta duƙufa wajan gina kasuwannin zamani

    04/02/2026 Duration: 09min

    Shirin   kasuwa akai miki dole na wannan makon  tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan gina kasuwanni na zamani da Gwamnatin Jihar Yobe ta sake ginawa a wasu sassan jihar domin karfafa harkokin kasuwanci da suka fuskanci koma baya, saboda matsaloli na Boko Haram. Shiga alamar sauti domin sauraron karin bayani.......

  • Yadda aka ƙulla yarjejeniyar kasuwanci mafi girma a duniya tsakanin India da EU

    28/01/2026 Duration: 10min

    Yau shirin ya mayar da hankali ne dangane gagarumar yarjejeniyar cinikayya mafi girma da ba’a taba ganin irinta ba, da aka cimma tsakanin ƙungiyar Tarayyar Turain ƙasar India. Yarjejeniyar da aka cimma yayin ziyarar da shugabannin Turai suka kai New Delhi na ƙasar India, za ta bada damar kasuwanci mara shinge tsakanin ƙasashe mambobin EU 27 da kuma ƙasar da ta fi yawan jama'a a duniya, waɗanda suka kaɗai suka mamaye kusan kashi 25% na jimillar hada-hadar kasuwancin cikin gida na duniya da kuma cinkayyar mutane biliyan biyu. Domin ko a shekarar 2024 kaɗai, an yi cinikin sama da Euro biliyan 120 a tsakanin ɓangarorin biyu. Masu sharhi na ganin cewa kalaman wannan yarjejeniya da ɓangarorin biyu suka cimma, alaƙa da manufofin Shugaban Amurka, Donald Trump, musamman duba da yadda Tarayyar Turai ke ƙoƙarin faɗaɗa abokan hulɗar kasuwancinta, ba tare da dogaro da Amurka kaɗai ba. Yarjejeniyar dai na nufin cewa daga yanzu, India za ta soke ko kuma zaftare haraji kan hajoji da dama da take shigarwa yankin Turai, da suk

  • Mahangar masana kan kiran IMF da bankin Duniya ga Najeriya don sauƙaƙa tsadar rayuwa

    21/01/2026 Duration: 10min

    Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole"na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan sabbin kiraye-kirayen da Bankin Duniya da kuma Asusun bada Lamuni na Duniya (IMF) suka yi ga gwamnatin Najeriya wajen ganin ta ɗauki matakab da suka kamata don ƙara rage hauhawar farashin kayayyaki domin al’umma ta amfana a zahiri da kuma ci gaban tattalin arziki ƙasar. Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Ƙasa da Ƙasa, IMF, sun bayyana cewa har yanzu tattalin arziƙin Najeriya bai kai matsayin da za a ce ya daidaita ba, duk da wasu sauye – sauye da gwamnati ke aiwatarwa. Hukumomin sun ce rashin daidaiton tattalin arziƙin na ci gaba da shafar rayuwar jama’a, musamman ta fuskar hauhawar farashin kayayyaki. Masana tattalin arziƙi sun goyi bayan gargadin da Asusun Ba da Lamuni na Ƙasa da Ƙasa, IMF, ya yi kan cewa sauye-sauyen tattalin arziƙin da ake aiwatarwa a ƙasashe masu tasowa, ciki har da Najeriya, na iya fuskantar barazana idan ba a tabbatar da dorewarsu ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Yadda Najeriya ta yi iƙirarin rarar tiriliyan 12 a watanni 6 farkon 2025

    14/01/2026 Duration: 10min

    Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan makon ya mayar da hankali kan ikirarin gwamnatn Najeriya na samun rarar kuɗi da ya kai tiriliyan 12 kuma kashi 21 daga ciki ta same su ne daga bangarorin da ba na man fetur ba a cikinn watanni 6 na farkon shekarar 2025. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Tasirin kama shugaba Maduro na Venezuela ga tattalin arzikin duniya

    07/01/2026 Duration: 10min

    Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya tattauna da masana da sauran masu ruwa da tsaki kan harkokin man fetir dangane da tasirin kama shugaban ƙasar Venezuela Nicolas Maduro da Amurka ta yi zai yi ga tattalin arzikin duniya.

  • Hangen masana tattalin arziƙi kan sabon harajin gwamnatin Najeriya

    24/12/2025 Duration: 10min

    Shirin "Duniya Akai Miki Dole" tare da Faruk Muhammad Yabo a wannan mako ya yi duba ne kan sabbin harajin da gwamnatin Najeriya ke shirin karɓa a hannun jama'ar ƙasar, a wani yanayi da ƙasar ke fatan tattara wani ɓangare na kuɗaɗen tafiyar da harkokinta. Shirin a wannan mako ci gaba ne na makon da ya gabata dangane da wannan dokar haraji wadda al'ummar Najeriya ke ci gaba da suka akanta. A cikin shirin akwai tattaunawa da ƙwararru a fagen na tattalin arziƙi waɗanda da dama suka yi suka ga sabon tsarin harajin na shugaba Tinubu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Abubuwan da sabon tsarin harajin Najeriya ya ƙunsa

    17/12/2025 Duration: 10min

    A wannan mako shirin zai tattauna ne kan sabuwar dokar harajin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanya wa hannu, wadda kamar yadda na ambata ba da jimawa, za ta fara aiki daga ranar 1 ga watan gobe na shekara mai zuwa. Tun a watan Yunin da ya gabata shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar harajin da ake sa ran za ta sauya fasalin tsarin karɓa da tattara kuɗaɗen shiga ga gwamnati daga ɓangaren haraji a Tarayyar Najeriya.

  • Al'ummar Nijar sun rungumi tsarin hada hadar kuɗi ta manhajar waya

    10/12/2025 Duration: 10min

    Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako ya leka Jamhuriyar Nijar ne, inda a shekarun baya bayan nan, hada hadar kuɗi ke neman yin ƙaura daga bankuna zuwa manhajojin wayar salula da ake kira da Mobile Money a Turance, da ake amfani da tsarin wajen aikewa da kuɗi ko karɓarsu a ciki da wajen ƙasar ta Nijar. Samun damar aika kuɗaɗe ta hanyar amfani da manhajojin wayar hannu ba tare da yankar kuɗin haraji masu dama ba, dai tuni ya kawo sauyi dangane da hada-hadar kuɗi a Jamhuriyar ta Nijar, lamarin da ya zo a daidai lokacin da aka takaita fitar da kuɗaɗe daga Bankuna bayan juyin Mulki, tsarin da ya sa mutane da dama masu asusun ajiya a bankuna rungumar mahajojin na zamani a matsayin sabbin wuraren adana kuɗaɗen nasu.  Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.........

page 1 from 2