Synopsis
Shirin yakan diba kasuwancida tattalin arizikin kasashen duniya ya ke ciki. Shirin yakan ji sabbin dubaru da hajojin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masanaantu dangane da halin da suke ciki.
Episodes
-
Yan Najeriya na yawaba Hasetins kan kafa kamfanin ma'adanai mafi girma a Afirka
03/12/2025 Duration: 10minShirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan gina katafaren kamfanin tono da kuma sarrafa ƙarafu da duwatsu masu daraja da wani matashi ya ƙaddamar a jihar Nasarawa da ke arewacin Najeriya, irinsa mafi girma a Afirka, wanda zai laƙume dalar Amurka miliyan 400.
-
Shin yaya harajin da bankuna ke cirewa ƴan Najeriya a asusunsu ke shafar tattalin arziki
19/11/2025 Duration: 10minShirin Kasuwa a kai Miki Dole na wannan mako ya mayar da hankali ne kan binciken da majalisar wakilan Najeriya ta ƙaddamar bayan ƙorafin ƴan ƙasar game da yawan haraji da bankuna ke cirewa a asusun su na ajiya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.
-
Majalisar wakilan Najeriya ta ƙaddamar da bincike kan yawaitar harajin Bankuna
12/11/2025 Duration: 10minA 'Kasuwa Akai Miki Dole' a wannan karon, ya mayar da hanhali ne kan binciken da Majalisar Walikan Nigeria ta ƙaddamar dangane da ƙorafin ƴan ƙasar kan maban-banta haraji da Bankuna ke yawaita cirewa a asusun ajiyarsu. A ƙarshen watan oktoban da ya gabata ne, Mjalisar Wakilan Najeriya ta kaddamar da wani kwamitin da ta dorawa alhakin bin diddigin korafe-korafen da masu ajiya a bankuna ke yi kan yawan cire musu kudade da ake yi daga asusun ajiyarsu na banki. Kaddamar da kwamitin, ya biyo bayan tarin korafe korafen da ƴan Nigeria ke yi, musamman masu ajiyar kudi a bankunan kasar, game da yawan cire musu kudade ba-gaira ba dalili da bankunan ke yi, da sunan wasu ayyuka da bankunan ke ikirarin gudanarwa. Masana na alakanta wannan batu, da nau’o’in harajin da ake da su a kasar, a matakin kananan hukumomi da jihohi da kuma tarayya, yayinda wasu ma’aikatan gwamnatin kasar, ke kukan cewa wasu kudaden da ake cire musu, musamman na gidaje da na pansho, ba a tura su ga hukumomin da suka dace. Ku latsa alamar sauti don s
-
Tasirin ƙarin harajin kashi 15 da Najeriya ta sanya kan man da ake shigarwa ƙasar
05/11/2025 Duration: 10minShirin a wannan makon ya yi dubi ne akan batun sabon harajin kashi 15 da gwamnatin Tarayyar Najeriya, ta sanya kan tataccen man fetur da dangogin sa da ake shigo da su ƙasar daga ketare, ala’marin da ya fara jefa fargaba a zukatan ƴan ƙasar kan yuwuwar tashin farashin litar man na fetur. A ranar Jumma’ar da ta gabata ce, fadar gwamnatin Najeriya, ta sanar da cewa tuni shugaban ƙasar Bola Tinubu ya amince da harajin fito na kashi 15 kan man fetir da dizal da za a shigo da su ƙasar daga waje, yana mai bayyana tsarin, a matsayin matakin bunƙasa matatun mai na cikin gida da kuma dogaro da kai a fannin makamashi. Sai dai, tuni dilllalan man fetur a ƙasar suka fara gargaɗin cewar muddin karin ya tabbata to akwai yuwuwar farashin man fetur da dangoginsa ya yi tashin da zai fi ƙarfin da yawa daga cikin al’ummar ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba...........