Taa Ka Lashe | Deutsche Welle

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 16:39:44
  • More information

Informações:

Synopsis

Muna gabatar muku da shirye-shirye masu ayatarwa da suka shafi al´adu da zamantakewa tsakanin al´ummomi da mabiya addinai daban-daban da nufin kyautata tsarin zamantakewa da fahimtar juna ta hanyar tuntuar juna da shawarwari tsakani ba tare da nuna fifiko akan wani ba.

Episodes

  • Taba Ka Lashe: Al'adar bikin aure a Guddiri

    15/03/2022 Duration: 09min

    Al'adar bikin aure a Guddiri a Jihar Bauchi dadaddiyar masarauta ce mai dumbin tarihi, kuma guddurawa suna da wasu fitattun al'adunsu da suka banbanta su da sauran masarautun Bauchi.

  • Taba Ka Lashe: 02.03.2022

    08/03/2022 Duration: 09min

    Ko har yanzu ana amfani da wakokin gargajiya da kayan kidan harshen Hausa a kasar Hausa? Shirin Taba Ka Lashe.

  • Taba Ka Lashe: Rayuwar Musulmi da Kirista

    15/02/2022 Duration: 09min

    Musulmi da Kirista a Jihar Filaton Najeriya na zaune a unguwani dabam-dabam sabanin yadda a baya al'ummomin biyu ke zaune wuri guda suna cudanya.

  • Taba Ka Lashe 02.01.2022

    08/02/2022 Duration: 09min

    Shirin na wannan lokaci ya yi nazari ne a kan kirari. Ya al'adar kirari take a kasashen Afirka?

  • Taba Ka Lashe: 26.01.2022

    01/02/2022 Duration: 09min

    Shirin na wannan lokaci ya ziyarci jihar Osun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya, inda ya gano wani Masallaci da ya kwashe shekaru aru-aru.

  • Taba Ka Lashe: 29.12.2021

    04/01/2022 Duration: 09min

    Ko kun san su wanene mafarauta da 'yan tauri da kuma yadda suke samun taurin? Ku saurari Shirin Taba Ka Lashe.

  • Taba Ka Lashe: 22.12.2021

    28/12/2021 Duration: 10min

    Shirin ya duba yunkurin farfardo da wata sarautar gargajiya ta kabilar Abzinawa a garin Afess na jahar Agadez a Nijar.

  • Taba Ka Lashe: 15.12.2021

    21/12/2021 Duration: 09min

    An gudanar da bikin nadin sababbin sarautu, a masarautar Hausawan Turai. Karin bayani cikin Taba Ka Lashe.

  • Taba Ka Lashe: 08.11.2021

    14/12/2021 Duration: 09min

    Mata na taka muhimmiyar rawa, wajen magance rikice-rikicen kabilanci da na addinai da makamantansu. Shirin Taba Ka Lashe.

  • Taba Ka Lashe: 24.11.2021

    30/11/2021 Duration: 09min

    Ko kun san yadda mabiya darikun Sufaye ke ziyara Kushewar Waliyai a Maroko? Shirin Taba Ka Lashe.

  • Taba Ka Lashe

    16/11/2021 Duration: 09min

    Wurin da ake tsugune da daruruwan mata da ake zargi da aikata maita a wata cibiya ta musamman da ake wa lakabi da "Sansanin mayu” a arewacin Ghana.

  • Taba Ka Lashe: 27.10.2021

    02/11/2021 Duration: 09min

    A duk ranakun 12 ga watan Rabi'ul Auwal na ko wacce shekara, al'ummar Musulmi a fadin duniya kan yi bukukuwan tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah Annabi Muhammad (SAAW). A wannan shirin mun yi nazarin yadda aka gudanar da bukukuwan na bana a jihar Kano da ke Najeriya.

  • Taba Ka Lashe 22.09.2021

    28/09/2021 Duration: 09min

    Yadda zamani ke shirin gusar da al'adun gargajiyan jahar Gaya a jamhuriyar Nijar. Latsa kasa don jin cikakken shirin.

  • Taba Ka Lashe: 15.09.2021

    21/09/2021 Duration: 10min

    Amfani da ahnnun hagu, halitta ce da daga Allah. Sai dai wasu na fuskantar kalubale sakamkon wasu al'adu da ma addinai. Ku saurari shirinmu na Taba Ka Lashe.

  • Taba Ka Lashe: 01.09.2021

    07/09/2021 Duration: 09min

    Ko kun san yadda kabilar Igbo da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, ke bikin binne gawa? Shirin Taba Ka Lashe.

  • Taba ka lashe 04.05.21

    31/08/2021 Duration: 09min

    Al'adar wasan kara a yankin Damagaram na Jamhuriyar Nijar wanda matasa ke yi a lokacin kaka bayan girbin amfani gona

  • Taba Ka Lashe: 11.08.21

    24/08/2021 Duration: 10min

    Ko kun san cewa akwai fadar Hauasawa har ma da sarkinsu a Turai? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari kan batun wannan sarauta.

  • Taba Ka Lashe: 04.08.2021

    10/08/2021 Duration: 09min

    Ko kuna da masaniya kan yadda al'adar wasan kara ke gudana a jihar Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar? Shirin Taba Ka Lashe

  • Taba Ka Lashe: 21.07.2021

    27/07/2021 Duration: 09min

    Shadi, dadaddiyar al'ada ce ta Fulani da aka fi amfani da ita wajen neman aure. Sai dai a yanzu al'amura sun sauya. Ko ya al'adar ta shadi take gudana a yanzu? Shirin Taba Ka Lashe.

  • Taba ka Lashe 21.07.2021

    20/07/2021 Duration: 09min

    Al'adar Sharo na fulani wata dadaddiyyar al'ada ce mai muhimmanci ga fulani wacce tun shekaru masu yawa suke yin ta musamman domin hada aure tsakanin samari da yan mata.

page 5 from 5