Dandalin Siyasa

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 7:41:09
  • More information

Informações:

Synopsis

Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan alamurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi alumma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.

Episodes

  • Ɗaukaka ƙara daga ADC za ta dakatar da hukuncin kotu kan Atiku da jamiyyar?

    Ɗaukaka ƙara daga ADC za ta dakatar da hukuncin kotu kan Atiku da jam'iyyar?

    07/11/2026 Duration: 20min

    A cikin shirin namu na yau, za mu ji cewa Babbar Kotun Tarayya ta soke shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark, tare da dukkan matakan da ya samar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar a zaɓen 2027. Za mu ji martanin Nafiu Bala Gombe, wanda ya shigar da ƙarar, da kuma martanin tawagar Atiku.

  • ADC ta magantu kan ikirarin da APC ta yi cewa Tinubu ya nada goyan bayan Arewa

    ADC ta magantu kan ikirarin da APC ta yi cewa Tinubu ya nada goyan bayan Arewa

    31/10/2026 Duration: 20min

    A cikin shirinmu na yau tare da Michael Kuduson za mu yi waiwaye akan babban gangamin fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya wanda shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar a Kaduna,, inda shugabannin jam’iyyar suka yi ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da goyon bayan Arewa. Za mu kuma ji martanin jam’iyyar ADC kan wannan ikirari, musamman batun cewa sama da mutum miliyan ɗaya ne suka halarci gangamin. Latsa alamar sauti don sauraron karin bayani.....

  • Ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan zargin INEC da saɓawa dokar zaɓe

    Ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan zargin INEC da saɓawa dokar zaɓe

    24/10/2026 Duration: 20min

    Shirin Dandalin Siyasa na wannan mako tare da Michael Kuduson ya yi duba kan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan zargin cewa Hukumar Zaɓen Najeriye, ta gaza wallafa rajistar masu zaɓe a intanet cikin wa’adin da dokar Zaɓe ta tanada. Sai dai hukumar ta ce ba ta karya doka ba. Latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....

  • Jamiiyyar APC ta kaddamar da majalisar yaƙin neman ta a hukumance

    Jami'iyyar APC ta kaddamar da majalisar yaƙin neman ta a hukumance

    17/10/2026 Duration: 20min

    Shirin dandalin Siyasa na wannan mako tare da Michael Kuduson ya mayar da hankali kan ƙaddamar da majalisar yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC, da kuma  martani akan zaɓen zaɓi jihar Kaduna a matsayin wurin fara gangamin Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....

  • Shirin ragin kuɗin man fetur na wata 1 ya janyo cece-kuce a Najeriya

    Shirin ragin kuɗin man fetur na wata 1 ya janyo cece-kuce a Najeriya

    10/10/2026 Duration: 20min

    Shirin ‘Dandalin Siyasa’ tare da Michael Kuduson a wannan mako ya yi duba ne kan matakin gwamnatin Najeriya kan shirin samar da rangwamen farashin man fetur na tsawon kwanaki 30, da martanin ’yan adawa. Sannan za mu waiwayi hukuncin Kotun Ƙoli da kuma matsayin Hukumar Zaɓen Najeriya, INEC, kan jam’iyyun siyasar da suka saɓa ƙa’idojin miƙa rajistar mambobinsu, da dai sauran batutuwan da muka tanadar muku a shirin. A daidai lokacin da ƴan Najeriya ke cigaba da kokawa kan tsadar rayuwa, musamman farashin man fetur da sufuri, gwamnatin ƙasar ta sanar da wani mataki na rage nauyin da ke kan al’umma. Gwamnatin ta ce za a sayar da man fetur bisa rangwame a gidajen mai na kamfanin man fetur na ƙasa, NNPC, na tsawon kwanaki 30, tare da bai wa masu jigilar fasinjoji fifiko. Sai dai mataki bai burge ƴan adawa ba, domin kuwa sun mayar da martani, inda suke ke tambaya ko rangwamen na ɗan lokaci zai iya magance matsalolin da suka shafi tsadar rayuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakke shirin.

  • Jawabin Tinubu na cika shekaru 66 da samun ƴancin kan Najeriya ya bar baya da ƙura

    Jawabin Tinubu na cika shekaru 66 da samun ƴancin kan Najeriya ya bar baya da ƙura

    03/10/2026 Duration: 20min

    Shirin ‘Dandalin Siyasa’ na wannan mako, ya maida hankali ne kan cikar Najeriya shekaru 66 da samun ƴancin kai, kuma yayin da ake bikin wannan rana, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ’yan ƙasar jawabi inda ya jaddada nasarorin da ya ce gwamnatinsa ta ce ta samu a fannin tattalin arziki, tare da bayyana fatansa na ganin ƙasar ta samu ƙarin wadata. Sai dai shugaban bai yi magana kan matsalar tsaro da ke ci gaba da ta zame wa wasu sassan ƙasar ƙarfen ƙafa ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson.............

  • A Najeriya shirin yaƙin neman zaben 2027 ya shiga wani sabon mataki

    A Najeriya shirin yaƙin neman zaben 2027 ya shiga wani sabon mataki

    12/09/2026 Duration: 20min

    Shirin na wannan makon tare da Michael Kuduson, ya yi nazari ne akan yadda a Najeriya yakin neman zaben 2027 ya shiga wani sabon mataki, bayan fara yakin neman zaben kujerun gwamna da ’yan majalisun jihohi a hukumance, inda Hukumar zabe ta Najeriya INEC ta kuma tunatar da ’yan takara da jam’iyyun siyasa cewa dole ne su gudanar da yakin neman zabe bisa tanade-tanaden doka.

  • INEC na duba yiwuwar gudanar da zaɓen gwaji na shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027

    INEC na duba yiwuwar gudanar da zaɓen gwaji na shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027

    05/09/2026 Duration: 20min

    Shirin na wannan makon, ya karkata ne kan yadda jam'iyyun siyasa ke ƙoƙarin cimma matsaya game da yadda za su tunkari zaɓen 2027, daidai lokacin da Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta INEC, na duba yiwuwar gudanar da zaɓen gwaji amma, na shugaban ƙasa, domin tantance shirye-shiryen tsarin zaɓen na baɗi. Wannan na zuwa ne, yayin da cikin makon jiya, aka jiyo Shugaba Bola Tinubu na bayyana cewa ɓangaren Arewacin ƙasar ne ya fi cin gajiyar wasu daga cikin sauye-sauyen da gwamnatinsa ta ƙaddamar, abin da ya fuskanci suka da caccaka daga masu ruwa da tsaki da ƙungiyoyin fararen hula. A gefe guda kuma, batun yadda ake tallafa wa jama'a a lokutan matsin tattalin arziki na cigaba da zama wani batu na siyasa, inda Ministan Tsaro ya yi kira ga gwamnonin jihohi da su daina raba babura a matsayin tallafin gaggawa ga jama'a, yana mai neman a mayar da hankali kan hanyoyin da za su samar da mafita mai ɗorewa. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson.

  • Ƴan adawa sun kaɗa hantar jamiyar APC mai mulki a Najeriya

    Ƴan adawa sun kaɗa hantar jam'iyar APC mai mulki a Najeriya

    29/08/2026 Duration: 20min

    Yayin da aka kaɗa gangar siyasa gabanin zaɓen shekarar 2027 da ke kara kusantowa, ƴan siyasa na ci gaba da gabatar da manufofi da alƙawuran da suke cewa za su inganta rayuwar ƴan Najeriya. A wannan makon, batun tallafin man fetur, sake bude iyakokin ƙasa da matsalar tsaro sun sake zama wasu daga cikin muhimman batutuwan da ƴan adawa ke amfani da su wajen ƙalubalantar gwamnati. Ku lasha alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson...........

  • Tasirin zaɓen gwamnan Osun ga babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027

    Tasirin zaɓen gwamnan Osun ga babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027

    15/08/2026 Duration: 19min

    Shirin Dandalin Siyasa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan tasirin zaɓen gwamnan jihar Osun yayin da ake tunkarar babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027. Shirin ya kuma yi duba game da halin da ake ciki a zaɓen na Osun, kama daga rikicin siyasa da kuma zarge-zargen da abokan hamayya ke yi wa juna. Latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin...

  • Muhawara ta dawo sabuwa kan cancantar shigar Malamai cikin Siyasa a Najeriya

    Muhawara ta dawo sabuwa kan cancantar shigar Malamai cikin Siyasa a Najeriya

    08/08/2026 Duration: 18min

    Shirin 'Dandalin Siyasa' na wannan makon ya tattauna ta Shiekh Dr Ahmad Mahmud Gumi kan matsayar da ya ɗauka ta goyon bayan bai wa Malamai damar shiga a dama da su a Siyasar Najeriya. Zalika shirin ya waiwayi ganawar da aka yi tsakanin Limaman Mujami'un Katolika da kuma shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnati.

  • INEC ta sha alwashin baiwa mara ɗa kunya a babban zaɓen Najeriya na 2027

    INEC ta sha alwashin baiwa mara ɗa kunya a babban zaɓen Najeriya na 2027

    01/08/2026 Duration: 20min

    Shirin ‘Dandalin Siyasa’ tare da Nura Ado Suleiman kamar kowanne mako a wannan karon ma ya yi duba kan manyan lamurran siyasar Najeriya har ma da wasu yankunan Yammacin Afirka. Sha’anin Siyasa a Najeriya dai na ci gaba da ɗaukar ɗumi la’akari da tun karar manyan zaɓukan da za su gudan a farkon shekara mai kamawa ta 2027.........zaben da ake cigaba da tafka muhawara kansa gami da bayyana ra’ayoyi a  tsakanin waɗanda ke da ƙwarin gwiwar zai sama karɓaɓɓe da kuma waɗanda ke ce wa da wuuya a ga wani sauyi. Wataƙila wannan batu ne ya sanya hukumar zaɓen Najeriya INEC shan alwashin bai wa maraɗa kunya...... Idan aka bi sannu a hankali za a ci tsokaci gami da mrtanin ƙwararru, ‘yan fafutuka da kuma sauran ‘yan Najeriya kan wannan lamari. Za mu kuma duba hukuncin da Kotun daukaka ƙara ta yi na yin watsi da buƙatar soke rijistar wasu jam’iyyun adawa a Najeriyar ciki har da ADC. A Kaduna kuwa gwamnan jihar Uba Sani ne ya kawo ƙarshen tsarin tikitin takarar Muslim Muslim da jam’iyyarsa ta APC ta shafe shekaru fiye da 10

  • Siyasar Najeriya ta ɗauki sabon salo dai dai lokacin da zaɓen 2027 ke tunƙarowa

    Siyasar Najeriya ta ɗauki sabon salo dai dai lokacin da zaɓen 2027 ke tunƙarowa

    25/07/2026 Duration: 20min

    Shirin Dandalin Siyasa na wannan makon tare da Michael Kuduson ya mayar da hankali kan yadda harkokin siyasa suka sake daukar sabon salo, inda Gwamnonin jihohin Kudu maso Gabas suka bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin sake tsayawa takara a zaben shekarar 2027 tare da jaddada aniyar taimaka wa cigaba da kasancewar Najeriya dunƙulallliyar ƙasa. A gefe guda kuma, rikicin siyasar Jihar Rivers ya sake daukar sabon salo bayan Gwamna Siminalayi Fubara ya nuna cikakken goyon baya ga yarjejeniyar sulhu da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike. Har ila yau, za mu duba muhawarar da ta biyo bayan sukar da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi kan yadda gwamnati ke ware kudade domin gyaran fadojin sarakuna, yayin da ake ci gaba da fuskantar kalubalen tattalin arziki. Sannan za mu yi nazari kan musayar zarge-zarge tsakanin Fadar Shugaban Kasa da Atiku Abubakar dangane da bayanan da suka shafi wasu tsofaffin shari'o'i a Amurka. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

  • Jamiyyun adawa na cikin rashin tabbas a Najeriya yayin da ake tinkarar zaɓen 2027

    Jam'iyyun adawa na cikin rashin tabbas a Najeriya yayin da ake tinkarar zaɓen 2027

    18/07/2026 Duration: 20min

    Shirin 'Dandalin Siyasa' na wannan makon tare da Micheal Kuduson ya mayar da hankali kan rashin tabbas da jam'iyyun adawa suka shiga a Najeriya, yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027. A wannan makon, wani hukunci da kotu ta yanke kan wasu taruka na jam’iyyar ADC, ya sake buɗe kafa ta tambayoyi kan yadda ake gudanar da harkokin cikin gida na jam’iyyu a Najeriya. Sai kuma batun jadawalin zaɓe na INEC, wanda kotu ta dawo da shi, abin da ya bai wa jam’iyyun siyasa damar cigaba da shirye-shiryensu bisa tsarin hukumar zaɓe.

  • Ƴan adawa a Najeriya sun ce ana yi musu barazana a fagen siyasar ƙasar

    Ƴan adawa a Najeriya sun ce ana yi musu barazana a fagen siyasar ƙasar

    11/07/2026 Duration: 20min

    A wannan makon, dan takarar shugaban ƙasa a Najeriya a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Peter Obi, ya yi ikirarin cewa rayuwarsa na cikin hadari, yana mai nuna damuwa kan yanayin siyasar kasar gabanin zaben 2027. A gefe guda kuma, rikicin shugabancin jam'iyyar ADC ya dauki sabon salo bayan wata kotu ta tabbatar da shugabancin Sanata David Mark, yayin da bangaren da ke adawa da wannan hukunci ke ci gaba da bayyana matsayinsa.

  • INEC ta ce kuɗaɗen da aka ware don gudanar da zaɓen 2027 ba su zo hannunta ba

    INEC ta ce kuɗaɗen da aka ware don gudanar da zaɓen 2027 ba su zo hannunta ba

    04/07/2026 Duration: 20min

    A wannan makon, hukumar zaɓe ta Njeriya,INEC, ta bayyana cewa har yanzu ba ta karɓi kuɗaɗen da aka tanadar domin fara shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027 ba. Wannan ya jawo martani daga ƙungiyoyin fararen hula, waɗanda ke ganin akwai abin da ya kamata a yi bayani a kai.

  • Halin da ake ciki game da babban zaɓen Najeriya da ke tafe

    Halin da ake ciki game da babban zaɓen Najeriya da ke tafe

    27/06/2026 Duration: 20min

    A wannan makon, shirin ya fara ne da matakin Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC, da ta bude shafinta na yanar gizo domin jam'iyyun siyasa su fara loda sunayen 'yan takararsu. Wani muhimmin mataki ne da ke nuna cewa shirye-shiryen babban zaben 2027 na kara daukar salo. Sai dai kuma, ba tsarin zabe kaɗai ake magana a kai ba, domin kuwa akwai batun tsaro bayan Majalisar Dattawa ta amince da kudirin kafa ƴan sandan jihohi. A gefe guda kuma, kotu ce a Najeriyar ta soke hukuncin da ya umarci Hukumar Zabe ta Kasa, INEC, ta yi wa jam'iyyar NDC rajista. Ko da yake wannan sabon hukunci na buƙatar ƙarin nazari daga ɓangarorin da abin ya shafa, abin da ke kara nuna cewa harkokin shari'a na cigaba da taka muhimmiyar rawa wajen tsara siyasar Najeriya gabanin zaɓen 2027. Idan aka cigaba da tsara yadda jam'iyyu za su shiga zaɓe, akwai kuma wata muhimmiyar tambaya: Idan lokacin zaɓe ya yi, wa zai tabbatar da tsaron ƴan takara, jami'an zaɓe da masu kaɗa kuri'a? Amsar wannan tambayar ta sake dawowa kan teburi bayan

  • Ta yaya Dimokraɗiyya zata sami karsashi a zaɓen Najeriya mai zuwa

    Ta yaya Dimokraɗiyya zata sami karsashi a zaɓen Najeriya mai zuwa

    20/06/2026 Duration: 20min

    Yayin da Najeriya ke kara tunkarar zaben 2027, ana cigaba da bayyana muhimman batutuwa da ke shafar yadda dimokaradiyya za ke gudana. Akwai batun da ya shafi dokokin zabe, inda wasu kungiyoyin farar hula ke cewa akwai wasu bangarori da ke haifar da tambayoyi kan adalci da daidaito. A daya bangaren kuma, akwai batun wani hukuncin kotu da ya kaɗa hantar jam’iyyun adawa, amma daga bisani wata babbar kotu ta yi watsi da shi. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson.

  • Yadda aka gudanar da bikin Ranar Dimokradiyya a Najeriya

    Yadda aka gudanar da bikin Ranar Dimokradiyya a Najeriya

    13/06/2026 Duration: 20min

    Shirin na wannan mako ya duba yadda Najeriya ta yi bikin Ranar Dimokaradiyya ta 12 ga watan Yuni, ranar da ake tunawa da gwagwarmayar tabbatar da mulkin dimokuradiyya da kuma muhimmancin kare ta. A jawabinsa ga kasa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya su ci gaba da kare dimokaradiyya duk da kalubalen da take fuskanta. Haka kuma ya yaba wa jami'an tsaro tare da kira ga 'yan ta'adda da masu daukar nauyinsu da su ajiye makamansu ko kuma su fuskanci fushin gwamnati. Shirin ya kuma duba yadda matsalar daba ke neman wuce gona da iri, wadda wasu 'yan siyasa ke amfani da ita, musamman a lokutan zaɓe. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson.

  • Zaɓen fidda gwanin Jamiyyar adawa ta ADC a Najeriya ya bar baya da ƙura

    Zaɓen fidda gwanin Jam'iyyar adawa ta ADC a Najeriya ya bar baya da ƙura

    30/05/2026 Duration: 20min

    Shirin 'Dandalin Siyasa' na wannan makon tare da Michael Kuduson, ya mayar da hankali a kan halin da siyasar jam’iyyun adawa ta shiga bayan gudanar zaɓen fidda gwani na jam’iyyar ADC don tsaida ɗan takarar shugabancin Najeriya, lamarin da ya bar baya da ƙura. Sakamakon zaɓen fidda gwanin na jami'yyar ADC dai ya haifar da rashin gamsuwa daga wasu ɓangarori a cikin jam’iyyar, waɗanda ke zargin cewa ba a cimma cikakkiyar fahimta ba kafin gudanar da zaben.

page 1 from 2